Shugaban kasar Masar Abdel-Fattah El-Sisi ya isa lardin Sichuan a ranar alhamis din nan 25 ga wata domin ziyarar aiki.
A lokacin ziyarar aiki na Abdel-Fattah El-Sisi a nan Kasar Sin sai da ya fara da Beijing fadar gwamnatin kasar tare da ganawa da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping sannan, kuma ya isa Sichuan a matsayin zangon sa na biyu. Ministocin kasar Masar da dama sun rufa masa baya a wannan karo. Ziyarar Shugaban na Masar nada zummar fahimtar tattalin arziki da al'ummar lardin Sichuan, da kara hadin kai tsakanin kasar sa da lardin. Ana sa ran bayan ziyarar sa a Sichuan, Abdel-Fattah El-Sisi zai ya koma Masar. (Amina)