Al-Ahwani ya ce tawagar shugaba Sisi mai kunshe da wakilan gwamnatin Masar, za ta tattauna da wakilan kasar Sin, game da wasu muhimman ayyuka, wadanda suka jibanci sassan biyu a yanzu da ma nan gaba.
Ya ce a halin yanzu kasar Sin ta zamo alkiblar kasashen duniya ta fuskar hadin gwiwa, kuma Masar na fatan karfafa wannan fanni yadda ya kamata. Kaza lika ministan ya bayyana kafa wani sashe na musamman, da zai rika kula da dangantakar hadin gwiwar Masar da kasar ta Sin.
Al-Ahwani ya kara da cewa sassan biyu na da kyakkyawar alaka. A hannu guda kuma Sin ta dade tana goyon bayan Masar a fannonin siyasa da na diflomasiyya, baya ga habakar hada-hadar cinikayya da zuba jari tsakanin sassan biyu.
Daga nan sai ministan ya bayyana burin kasar sa, na daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin kau da duk wani yanayi, da ka iya zamowa matsala ga ci gaban harkokin cinikayya, da na zuba jari a kasar.(Saminu)