in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gabatar da karar tona sirrin kasa kan Mohamed Morsi
2014-09-07 16:58:48 cri
A Masar an gabatar da wata kara dake bukatar a hukunta tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi bisa zargin cin amanar kasa.

Hukumar gabatar da kararraki ta kasar ce ta gabatar da wannan korafi gaban kuliya a jiya Asabar, tana mai zargin Morsi da aikata laifuka masu alaka da tona sirrin kasar ga kasar Qatar.

Wata sanarwa da babban mai gabatar da kara a kotun kasar ta Masar Hesham Barakat ya fitar, ta ce Morsi da wasu jami'ai 9, sun fidda bayanan sirrin gwamnati, da na hukumar tsaron kasar ta Masar ga kasar Qatar, ta kafar gidan talabijin na Al-Jazeera wanda hedkwatarsa ke kasar Qatar.

Haka kuma, mahukunatan kasar ta Masar sun fidda wasu bayanan dake zargin tsohon shugaba Morsi, da sauran mutanen su 9, da tona sirrikan harkokin sojojin kasar, da na babbar hukumar leken asiri da wasu karin manyan hukumomin kasar.

Ya zuwa yanzu dai ba a sanya ranar fara wannan shari'a ba.

Har wa yau, baya ga batun tona sirrin kasa da aka yi wa Mohamed Morsi, a daya bangaren an zarge shi da hada kai da wasu bangarori daga ketare, domin shirya husuma tsakanin al'umma'ar kasa, wanda hakan ya kai ga kisan masu zanga-zanga da kuma fasa gidan yari.

Sai dai a nasa bangare Mohamed Morsi ya yi watsi da dukkanin zarge-zargen da aka yi masa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China