Jami'an sun bayyana hakan ne dai a jiya Asabar a birnin Alkahira na kasar Masar ya yin wani taron manema labaru na hadin gwiwa da suka gudanar.
Da yake karin haske game da hakan, mista Shoukry ya ce Masar na goyon bayan Amurka a fagen yaki da kungiyar ISIS, da ma sauran kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi, ta na kuma kira ga sauran kasashen duniya da su goyi bayan wannan kuduri domin cimma nasarar yaki da masu tsattsauran ra'ayi.
A wani ci gaban kuma Mr. Kerry ya gana da shugaban Masar Abdelfattah al Sisi, da babban sakataren kungiyar tarayyar kasashen Larabawa Nabil el-Araby, inda a zantawarsa da shuwagabannin biyu, shugabannin sun nuna cewa, kamata ya yi a kara zage damtse wajen karfafa yakin da ake yi da kungiyoyin 'yan ta'adda.(Fatima)