Xi Jinping ya nuna cewa, kasancewarta babbar kasa a tsakanin kasashen Larabawa, Afrika da Islama da kuma kasashe masu tasowa, kasar Masar da Sin sun fahimci juna da mutunta juna tare kuma da amincewa har ma da goyan bayan juna ,abin da yasa hakan dangantakar dake tsakanin Sin da Masar ta kasance abin koyi ga sauran kasashen Larabawa, kasashen Afrika da kuma tsakanin kasashe masu tasowa. Sin kuma tana dora babban muhimmanci kan huldar da ke tsakaninta da kasar ta Masar.
A nasa bangare shugaba Sisi ya ce, Masar na kokarin tabbatar da zaman karko da bunkasuwar tattalin arziki, don haka tana fatan raya dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin a dukkanin fannoni, har ma da zurfafa hadin kai tsakanin kasashen biyu ta fuskar siyasa, tattalin arziki, al'adu, aikin soja, tsaro da sauransu.
Bayan ganawar, shugabannin biyu sun daddale yarjejeniyar kafa dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni da kuma ganewa idanunsu yadda aka sa hannu kan wasu yarjejeniyoyi ta fuskokin tattalin arziki, ciniki, aikin zirga-zirga a sararin samaniya, makamashi da sauransu. (Amina)