A ran 24 ga wata, an kai harin boma-boman da aka dana cikin motoci a wata tashar binciken soja dake lardin Sinai na arewa na kasar Masar, wanda ya zuwa yanzu, ya haddasa rasuwar sojojin kasar a kalla 30, yayin da wasu suka jikkata.
Dangane da lamarin, shugaban kasar Masar Abdelfattah al Sisi ya sa hannu kan wani kuduri a wannan rana da dare, inda ya sanar da cewa, tun ranar 25 ga wata, wasu wuraren dake arewacin lardin Sinai za su shiga yanayin ko ta kwana na watanni uku, a lokacin, za a kafa dokar hana fitar dare a wuraren tun karfe biyar na dare zuwa karfe bakwai na safe a ko wace rana.
Bugu da kari, ta bakin kakakinsa, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa a ran 24 ga wata da dare, inda ya yi alla wadai da harin ta'addanci da aka kai a lardin a wannan rana. (Maryam)