Ta yiwu Mohammed Morsi ya fuskanci hukuncin kisa bisa zargin tona asirin kasar
Rahotanni daga Masar na nuni da cewar, akwai yiwuwar tsohon hambararren shugaban kasar Masar Mohammed Morsi, zai fuskanci hukuncin kisa bisa zargin tona asiri tare da mika wadansu mihimman takardu masu nasaba da tsaron kasar ta Masar ga gidan talabijin na kasar Qatar Al-jazeera wanda ke da babban ofishinsa a Doha.
Kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA, ya ruwaito cewar wata majiya ta shari’a ta ce tsohon hambararren shugaban kasar da wadansu mutane 10, za su fuskanci tuhuma a bisa laifin mika mahimman fayilolin tsaron kasar ga kasar Qatar a bisa umurnin kungiyar ‘yanuwa musulmi ta duniya.
Babban Lauyan Gwamnatin kasar ta Masar ya gabatar da jerin laifuka da ake zargin Morsi ciki har da wasu laifuka da za’a iya yankewa hambararren shugaban kasar hukuncin kisa a karkashin dokar kasar.
Tun dai a shekarar 2013 ne hulda tsakanin Qatar da kasar Misra ta yi tsami bayan da sojojin kasar suka hambarar da gwamnatin Morsi, kuma tuni kasar Masar ta yi shelar cewar kungiyar ‘yan uwa musulmi kungiya ce ta ‘yan ta’adda. (Suwaiba)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku