Kotun ta kuma kori shari'ar da ake yi wa wasu manyan jami'an tsohuwar gwamnatin tasa, ciki hadda tsohon ministan cikin gida na gwamnatin Habeb Al-Adly, da karin wasu jami'an su 6 da aka zarga da ba da umarnin kisan masu boren.
Baya ga batun kisan masu zanga-zangar, kotun ta kuma wanke Mubarak da ministan mai a gwamnatinsa daga zargin aikata cin hanci, mai alaka da iskar gas da Masar din ta fitar zuwa Isra'ila a wancan lokaci.
A shekarar 2012 ne dai wata kotun hukunta manyan laifuffuka a kasar ta yanke wa Mubarak hukuncin na daurin rai da rai, kafin daga bisani ya daukaka kara.
Shugaba Mubarak wanda a yanzu haka ke zaman jarun na shekaru 3, sakamako wani laifi na cin hanci da rashawa, shi ne shugaban kasar Masar na farko da aka zartaswa hukunci a shari'ar da aka shafe shekaru 4 ana gudanarwa. (Saminu Alhassan)