A lokacin ganawar, firaminista Li ya bayyana cewa, akwai dankon zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu cikin dogon lokaci, wadanda suka yi ta taimakawa juna. A jiya, shugaba Xi Jinping ya yi shawarwari da shugaba El-Sisi tare da samun sakamako mai kyau. Sin na fatan yin kokari tare da Masar, a kokarin bunkasa dangantaka tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.
A nasa bangare, shugaba El-Sisi ya yaba bisa ga manufar diplomasiyya da Sin take bi, kuma ya nuna girmamawa ga babban sakamakon da Sin ta samu a fannin bunkasuwa. A don haka Yace kasar Masar na fatan karfafa hadin gwiwa tsakaninta da Sin a duk fannoni, musamman ma a fannonin makamashi, zuba jari da sauransu. Tana kuma maraba da kamfanonin Sin da su shiga manyan ayyuka na kasar, a kokarin samun karin ci gaba a fannin hadin gwiwa da raya dangantaka tsakaninsu.
Bayan haka, a wannan rana kuma, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang ya gana da shugaba El-Sisi.(Fatima)