Jami'in hukumar tsaron kasar ya bayyana wa 'yan jarida cewa, an kai hari kan motar soja wadda ke aikin kiyaye tsaro a dab da wata tashar samar da iskar gas dake birnin Al-Arish na jihar North Sinai ta zirin Sinai a wannan rana, wanda ya haddasa mutuwa da raunata wasu sojoji. Ya zuwa yanzu, babu wata kungiyar da ta sanar da daukar alhaki kan wannan lamari.
Tun bayan da sojojin kasar suka sauke tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi daga mulkinsa a watan Yuli na bara, halin tsaro da ake ciki a kasar ya tsananta, kuma a kan samun rikice-rikice da hare-hare a kasar. Bisa kididdigar da gwamnatin kasar ta yi, an ce, lamuran tashe-tashen hankali da aka tayar tun daga watan Yuli na bara sun haddasa mutuwar mutane kimanin dari 5, yawancinsu kuwa sojoji ne da 'yan sanda.
A halin yanzu, sojojin kasar Masar na ci gaba da daukar matakan soja ga masu tsattsauran ra'ayi dake zirin Sinai. (Zainab)