Bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaba Abdel Fattah el-Sisi zai kawo ziyarar aiki kasar Sin ranar 22 zuwa 25 ga wata, kuma wannan ita ce ziyarar aiki ta farko da shugaba el-Sisi zai kawo kasar Sin tun bayan da ya hau karagar mulkin kasar.
Abdel Fattah el-Sisi ya ce, zai yi amfani da wannan ziyara wajen karfafa dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin, tare da janyo karin hankulan kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a kasar.
Bugu da kari, ya jaddada cewa, ya kamata a raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa ka'idojin neman bunkasuwa da kuma kiyaye zaman lafiya, ta yadda zai dace da moriyar jama'ar kasashen biyu. (Maryam)