Yayin babban taron MDD karo na 69 a wannan rana, an yi taron musamman kan yadda cutar Ebola ke yaduwa, inda Wang Min ya bayyana cewa, ya kamata a kara taimakon da za a baiwa kasashen yammacin Afirka da abin ya shafa dangane da yanayin da suke ciki a halin yanzu, kuma a cika alkawarin da aka yi musu yadda ya kamata. Ya kamata a gaggauta kafa da kyautata ayyukan tattara da nazarin bayanai game da yanayin yaduwar cutar, da kuma taimaka wa kasashen Afirka kan yadda za su karfafa ayyukansu na kiwon lafiya.
Ya kuma kara da cewa, jama'ar kasar Sin na son tsayawa tare da jama'ar yammacin kasashen Afirka wajen yaki da cutar Ebola, wannan ya sa, kasar ta Sin ta samar wa kasashen da abin ya shafa taimakon gaggawa sau da dama, kuma tana daya daga cikin kasashe na farko da suka fara baiwa kasashen dake fama da cutar Ebola taimako, ciki had da taimakon kudade da na kayayyakin agaji, Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta kammala zagaye na uku na kayayyakin taimakon da ta yi alkawarin bayarwa, da suka kai jimillar RMB Yuan miliyan 750, ciki hada da taimakon kudi na dallar Amurka miliyan 6 da ta samar wa hadadden asusun amintattu na yaki da cutar Ebola na MDD, kana tana ci gaba da gudanar da harkokin taimako zagaye na hudu. (Maryam)