Shugaba Putin ya bayyana haka ne yayin wata liyafar cin abincin dare ta ranar ma'aikatan hukumomin tsaron kasa ta Rasha, da ta gudana a fadar Kremlin jiya Asabar.
Putin ya ce ana cikin wani muwuyacin hali game da huldodin kasashen duniya, ya yin da Rasha ke ci gaba da fuskantar karin kalubale sakamakon watsi da aka yi da dokokin kasa da kasa.
A daya bangaren kuma shugaba Putin ya ce a bana kadai, an samu nasarar dakile wasu ayyukan ta'addanci guda 60 a kasar ta Rasha, an kuma hallaka kungiyoyin ta'addanci, da na masu tsattsauran ra'ayi 46.
Daga nan sai ya yi kira ga dukkanin jami'an hukumomin tsaron kasar, da su kara mai da hankali kan ayyukansu, su kuma karfafa hadin gwiwa tare da sauran hukumomi masu alaka, wajen yaki da ta'addanci, da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da dai sauransu. (Maryam)