A yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana cewa, a watanni biyu da suka gabata, shi da Medvedev sun tattauna da juna a yayin ganawa ta lokaci-lokaci karo na 19 a tsakanin firaministocin kasashen biyu a birnin Moscow. Yanzu gwamnatocin kasashen biyu suna kokarin aiwatar da ra'ayoyin bai daya da suka cimma ta fuskar hadin gwiwarsu a ganawar, da kuma raya dangantakar abokantaka a tsakaninsu daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare.
Kana Li Keqiang ya yi nuni da cewa, kasar Sin na da aniyar inganta hadin gwiwa tare da kasar Rasha a fannonin makamashi da layin dogo mai saurin tafiya. Kuma yana fatan kasashen biyu su kara taimakawa juna a yankin gabas na kasar Rasha. Hakazalika, kasar Sin tana son tattaunawa da Rasha domin neman hadin kansu a fannin da ba na makamashi ba musamman ma a fannin raya ayyukan more rayuwa.
A nasa bangare, Mr. Medvedev ya bayyana cewa, kasar Rasha tana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannonin da suka shafi man fetur, iskar gas, makamashin nukiliya, samar da wutar lantarki ta karfin ruwa, hada-hadar kudi, kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, kera jiragen sama, bincike kan sararin samaniya da dai sauransu.(Zainab)