Shugaba Putin wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labaru da aka gudanar a birnin Moscow dake kasar Rasha, ya kara da cewa kasar Sin abokiya ce mafi girma ga Rasha a fannonin tattalin arziki da ciniki. Kana muhimmin aikin dake gaban bangarorin biyu shi ne, inganta hadin gwiwar tattalin arziki, da ciniki tsakanin kasashen biyu a dukkanin fannoni, musamman ma batun kara fadada hadin gwiwa a fannin fasahohin zamani.
Kaza lika Putin ya bayyana cewa, kasashen Rasha da Sin suna da damar cimma moriya iri daya a fannoni da dama, kuma babu shakka hadin gwiwarsu a kwamitin sulhun MDD, zai kasance muhimmin mataki da zai tabbatar da yanayin da ake ciki a duniya.
Wakilan kafofin watsa labaru fiye da 1200 ne dai suka halarci wannan taron manema labaru na fadar gwamnatin Rasha. (Zainab)