Shugabannin sun tattauna ne dai kan batutuwan da suka shafi dangantakar kasashen biyu, da kuma halin da ake ciki a gabashin kasar Ukraine.
Kafin zantawar tasu a ranar Laraba wasu kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, yayin zantawar shugaba Putin ya yi wasu kalamai na barazana ga shugaba Poroshenko, sai dai babban sakataren harkokin watsa labaran shugaban Dmitri Peskov, ya yi watsi da wannan batu, yana mai cewa ko alama batun ba shi da tushe bare makama.
An dai ce shugabannin sun tattaunawa kan dangantakar kasashen nasu da yanayin da gabashin kasar Ukraine ke ciki, kuma shawarwarin da suka gudanar na da matukar amfani a kokarin da ake yi na warware matsalar kasar Ukraine. (Maryam)