Dangane da hakan, Mr. Lukashevich, ya ce a hakika daftarin wanda shugaba Obama ya gabatar, ba shi da nufin marawa kasar ta Ukraine baya, sai dai kawai wata manufa ta kalubalantar Rasha, lamarin da ya sa Rashan yin watsi da shi.
Har ila yau Lukashevich ya ce daftarin ya nuna matsayin masu rike da madafun ikon kafa dokokin Amurka, na burin yanke dangantakar dake tsakanin kasarsu da Rasha na tsahon lokaci.
A wani ci gaban kuma shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce manufofin kasarsa game da harkokin soja ba su canja ba, kuma Rashan za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka, wajen kiyaye tsaron kanta, tare da kiyaye moriya da ikon mulkin kasar, tare da dukufa wajen karfafa zaman lafiyar kasa da kasa. Kana Rasha na da fatan dukkanin kasashen duniya da al'ummominsu, za su cimma burin wanzuwar yanayin tsaro na bai daya. (Maryam)