Ya kuma kara da cewa, ministan harkokin wajen kasarsa Sergei Lavrov da takwaransa na kasar Amurka John Kerry za su gana a birnin Rome a ran 14 ga wata, inda za su tattauna yanayin Gabas ta Tsakiya. Haka kuma, mai iyuwa ne, Sergei Lavrov zai ambaci daftarin goyon bayan Ukraine wajen samun 'yancin kai da majalisar dokoki ta kasar Amurka ta zartas da shi kwanan baya. Sabo da a ganin kasar Rasha, daftarin ya nuna kiyayar da Amurka take nunawa kasar Rasha, a sa'i daya kuma, ya nuna cewa, kasar Amurka tana bukatar Rasha da ta amince da wani kudurin da bai nuna adalci ga kasarta. An zartas da daftarin goyon bayan kasar Ukraine wajen samun 'yancin kai a ran 11 ga wata a majalisar dattawan Amurka, inda Amurka za ta mai da kasashen Ukraine, Georgia da kuma Moldova a matsayin abokan hada kai nata, kuma za ta ci gaba da kakaba wa kamfanonin fitar da masana'antun iskar gas da hajojin tsaron kasar Rasha karin takunkumi. (Maryam)