Wannan batu dai na zuwa ne, bayan da mataimakin shugaban cibiyar kula da halin da ake ciki game da dokar ta baci na kasar Rasha Oleg Voronov ya bayyana cewa, sai da jami'an kwastam na Ukraine suka tantance kayayyakin jin kai, a tashar Matveyev kurgan, da ta Donetsk dake iyakar kasar da Rasha, sannan ayarin motocin dake dauke da kayayyakin suka shiga kasar Ukraine.
Sai dai a daya hannun kakakin kwamitin tsaron kasar Ukraine Andriy Lysenko ya bayyana cewa, kasancewar wakilin kungiyar Red Cross bai halarci aikin jigilar kayayyakin da Rashan ta samar ba, ya sa ma'aikatan kwastam na Ukraine kauracewa bincikar kayayyakin.
Kaza lika Lysenko ya kara da cewa, ayarin kayayyakin da Rasha ta shigar, ba za su biya hakikanin bukatun jama'ar dake gabashin kasar ta Ukraine ba. (Zainab)