A ranar 13 ga wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwaran aikinsa na kasar Rasha Dmitry Medvedev sun yi shawarwari yayin taron firaministocin Sin da Rasha karo na 19.
A gun shawarwarin, Li Keqiang ya bayyana cewa, shugabannin kasashen biyu sun yi ganawa sau da dama a wannan shekara, kana firaministocin kasashen biyu sun yi shawarwari sau 19 a tsakaninsu, wannan ya bayyana cewa, an raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare a dogon lokaci. Kuma kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Rasha wajen inganta hadin gwiwar dake kasashen biyu, da samun sakamakon hadin gwiwa mai amfani ta hanyar raya dangantakar abokantakar dake tsakanin kasashen biyu don amfanawa kasashen biyu da jama'arsu, har ma da sa kaimi ga samun zaman lafiya da farfadowar tattalin arziki a fadin duniya.
Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana son kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Rasha a fannonin tattalin arziki da cinikayya don cimma burin samun kudin da ya kai dala biliyan 100 daga ciniki a tsakaninsu a shekarar 2015, da kara yin hadin gwiwa a fannonin hakar ma'adinai, da sinadirai, aikin gona, ayyukan more rayuwa da dai sauransu, da kara zuba jari ga juna, da zurfafa hadin gwiwa a fannin raya makamashin nukiliya da sauran makamashi baki daya, da kara sa lura kan mu'amalar al'adu dake tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangare, Medvedev ya bayyana cewa, kasar Rasha tana son yin kokari tare da kasar Sin wajen yin amfani da fifikonsu a fannin bunkasuwar tattalin arziki, da sa kaimi don ganin an zuba jari ga juna, da kara yin hadin gwiwar yin nazari da samar da kayayyaki, da samar da kayayyakin more rayuwa a fannin sufuri, kamar jiragen sama, don inganta dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
Bayan yin shawarwarin, firaministocin kasashen biyu sun daddale hadaddiyar sanarwar bayan shawarwari karo na 19 a tsakanin firaministocin Sin da Rasha, tare da kallo da sa hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin tattalin arziki, cinikayya, zuba jari, makamashi, hada-hadar kudi, fasahohin zamani, al'adu da dai sauransu. (Zainab)