Shugaba Putin ya bayyana haka ne a yayin taron ci gaba da karfafa ayyukan soja na kasar Rasha da ya gudana a jiya Laraba. Shugaban na Rasha ya kuma bayyana cewa, ko da yake wasu kasashe na son shigar da kasar Rasha cikin makarkashiyar siyasar yanki da suke shiryawa, a hannu guda Rashan ba za ta amince da hakan ba.
Dangane da haka, a matsayin sa na jagoran rundunar sojan kasar ta Rasha, Putin ya yi kira ga dukkanin bangarorin sojin kasarsa, da su dukufa wajen kiyaye mulkin kai, da kuma cikakken yankin kasar gami da na kasashen dake kawance da ita.
Shugaba Putin ya kuma jaddada cewa, kamata ya yi hukumomin kasar dake kula da harkokin tsaron, su karfafa mu'amala da hadin gwiwarsu wajen warware batutuwan masu alaka da hakan. (Maryam)