Lavrov ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Syria Walid Muallem. Ya ce yanzu gwamnatin kasar Syria ta riga ta kammala aikin lalata makamanta masu guba, wanda hakan ke nuna tana da burin yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya kan wasu muhimman batutuwa.
Ban da wannan kuma, Lavrov ya ce, kasar Rasha za ta ci gaba da samar da gudummawa ga gwamnatin kasar Syria, a fagen karfafa yaki da ta'addanci, da ci gaba da raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu, domin cimma burin kawar da ta'addanci a yankin gabas ta tsakiya. (Zainab)