Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi yayin ganawarsa da shugaba Vladimir Putin na Rasha, ya ce kamata ya yi alakar sassan biyu ta zamo kan gaba cikin manufofin diflomasiyyarsu, duk kuwa da irin sauye-sauyen da ake samu game da huldodin kasashen duniya.
Har wa yau shugaban kasar ta Sin ya bayyana irin ci gaban da kasashen biyu suka samu a fannin tsara manufofin hadin gwiwa, lamarin da ya danganta da dorewar tattaunawa tsakanin kasashen biyu.
Daga nan sai ya bayyana burin da aka sanya gaba game da hadin gwiwar Sin da Rasha, wajen gudanar da bincike, da bunkasa ci gabansu daga dukkanin fannoni.
Bugu da kari shugaba Xi ya jinjinawa irin nasarar da ake samu game da musayar fasahohi tsakanin al'ummun sassan biyu, baya ga karin kusanci da hadin kai, tare da tafiya bai daya da kasashen biyu ke samu game da harkokin da suka jibanci kasa da kasa.