in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha tana mutunta kudurin al'ummar gabashin Ukraine a lokacin zabe
2014-11-03 10:34:26 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha a jiya Lahadi 2 ga wata ta ce, tana mutunta kudurin da al'ummar kudu maso gabashin Ukraine suka bayyana ta zaben shugabannin yankunan da wakilan majalissar dokoki.

A cikin wata sanarwa wadda ta ce, zaben na yankunan Donetsk da Lugansk gaba daya an yi su bisa tsari, kuma jama'a sun fito matuka, ta bayyana cewa, wadanda aka zaba sun sami amincewar al'umma ta dawo da zaman lafiya da wadata a yankin.

A cikin wata sanarwa da shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya fitar a wannan rana ta Lahadi, ya kira zabukan da aka yi a wadannan wurare biyu da sunan magudi yana mai cewa, fatan shi shi ne al'ummar Rasha ba za su amince da zaben ba saboda karara ya nuna sabawa daftarin Minsk na 5 ga watan Satumba wanda kuma wakilan kasar suka rattaba wa hannu.

Daftarin Minsk dai wata yarjejeniya ce ta kasa da kasa da aka amince da shi domin kawo karshen kai ruwa rana da ake ta yi tsakanin 'yan aware da dakarun gwamnatin Ukraine.

An dai fara kada kuri'an ne da misalin karfe 8 da safiyar wannan rana zuwa 8 na dare inda 'yan takara 3 suka fito neman shugabancin yankin Donetsk, sannan 'yan takara 4 kuma suka tsaya neman shugabancin yankin Lugansk. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China