Ban da haka kuma, Lavrov ya zargi kasar Amurka da rashin mai da hankali kan tsari na bar jama'ar wata kasa su yanke shawara, musamman ma a wata kasa mai 'yancin kai wadda ke zama karkashin kulawar kundin MDD, sai dai maimakon bin wannan tsari, kasar Amurka tana kokarin nuna wa sauran kasashe abin da ya kamata a yi. A cewar Lavrov, duk da cewa matakan soja da Amurka ta dauka a shekaru baya sun yi barna sosai, amma ba ta so ta canza manufarta, har zuwa yanzu Amurka tana ci gaba da kokarin gudanar da matakan soja da tsoma baki cikin harkokin sauran kasashe. (Bello Wang)