in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin ta kafa shirin musammun na yaki da cututtukan da ba su yaduwa
2014-06-05 11:01:56 cri

Kasar Benin ta cimma wani shirin musammun na yaki da cututtukan da ba su yaduwa ga mutane daga bakin shekarar 2014 zuwa shekarar 2018, domin tabbatar da rigakafi da daukar nauyin wadannan cututtuka yadda ya kamata, a wani labarin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu daga hukumomin kasar a ranar Laraba a birnin Cotonou.

Shirin na musammun na yaki da cututtukan da ba su yaduwa ga mutane, na a matsayin wani tsarin kasancewa wani misali kan ayyukan da cibiyar kasa ta yaki da cututtukan da ba su yaduwa ga mutane za ta gudana daga shekarar 2014 zuwa shekarar 2018 domin yin rigakafin irin wadannan cututtuka, ta yadda za'a iyar tabbatar da samar da jinya ga mutane yadda ya kamata, in ji ministar kiwon lafiyar kasar Benin, madam Dorothee Kinde Gazard. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China