Rahoton ya nuna cewa, tun daga shekarar 1980 zuwa shekarar 2008, yawan mutane masu kiba a kasashen da suka ci gaba ya karu da kashi 75 bisa dari, yayin da adadin ya kai kashi 260 bisa dari cikin kasashe masu tasowa, lamarin ya kawo damuwa sosai. Kuma, adadin mutane masu kiba a kasar Sin da kasar Mexico ya kusa ninka sau biyu, yayin da adadin ya ninka kashi 1 bisa 3 a kasar Afrika ta Kudu.
Rahoton ya kuma nuna cewa, dalilin da ya sa haka shi ne, domin yawan cin sukari da gishiri da jama'ar kasashe masu tasowa suke yi a cikin zaman rayuwar yau da kullum, bisa karuwar kudaden da suka samu da kuma bunkasuwar birane a wandannan kasashe. Ban da wannan kuma, cika cin abinci ba tare da motsa jiki ba shi ma na daya daga cikin dalilan da suka sanya haka. (Maryam)