in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta cimma wani shirin kare kananan yara nan da karshen shekarar 2015
2014-04-09 10:46:06 cri

Kasar Kenya tana hangen kafa wani shirin kare kananan yara nan da karshen shekarar 2015, in ji ministan kiwon lafiyar kasar.

Jami'ar dake kula da ayyukan kiwon lafiyar jarirai, kananan yara da 'yan mata a ma'aikatar kiwon lafiya, madam Rachel Nyamai ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Nairobi cewa, bangarorin da abin ya sha suna bincike a yanzu haka kan wannan shiri kafin ya samu amincewar gwamnatin kasar.

Wannan shiri yana da manufar kara adadin kara ceto rayuwar kananan yara a cikin kasar, in ji madam Nyamai a yayin bikin kaddamar da shirin kungiyar kiwon lafiyar kananan yara ta Kenya a birnin Nairobi.

Haka kuma wannan shiri zai samar da hanyoyin sanya ido na ganin cewa, ko wane yaro zai samu damar nuna kwarewarsa ta ko wane fannin zaman rayuwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China