in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Afrika na tattara dala miliyan 700 domin kyautata kiwon lafiya
2014-05-09 10:10:38 cri

Yawan kudaden da kasashen Afrika za su kebewa shirin kamfe yin allurar rigakafin cututtuka zai karu har zuwa kimanin dalar Amurka miliyan 700 tsakanin shekarar 2016 zuwa shekarar 2020, idan aka kwatanta da dalar Amurka miliyan 254 da ake zuba wajen irin wannan aiki tsakanin shekarar 2011 zuwa shekarar 2015.

Wannan shiri na cikin yanayin alkawuran da shugabannin kasashen Afrika da suke dauka na taikamawa tsare-tsaren gudanar da kamfen allura cikin dogon lokaci bisa shirinsu na zuba jari domin tabbatar da lafiyar kananan yara da iyalai a cikin kasashensu a nan gaba.

Wadannan alkawura, an gabatar da su a albarkacin sanarwar "shirin allurar rigakafi a Afrika a shekarar 2020" a ranar Alhamis a birnin Abuja, da aka fitar a yayin dandalin tattalin arzikin duniya kan Afrika.

Wannan alkawari na nuna mai da hankali sosai na shugabannin Afrika game da muhimmancin da suke baiwa kiwon lafiyar kananan yara a Afrika, in ji Jakaya Kikwete, shugaban kasar Tanzaniya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China