A yayin ganawar, shugaba Xi ya bayyana cewa, yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka ta fuskar kiwon lafiya, wani muhimmin bangare ne na hadin gwiwar da ke tsakaninsu. Yana fatan taron zai ba da gudummowa wajen kara azama kan yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a fannin kiwon lafiya, da tabbatar da lafiyar jama'ar Sin da Afirka, bisa tsarin taron dandalin tattaunawar yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka.
Har wa yau shugaban ya nuna godiya kan gudummowar da kungiyoyin kasa da kasa suka bayar kan goyon bayan ayyukan kiwon lafiya na Sin da Afirka, da tabbatar da adalci a duk duniya ta fuskar kiwon lafiya. Ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da mara musu baya, da kuma goyon bayan kasashen Afirka da su tabbatar da manufar bunkasuwa da MDD ta tsara a shekarar 2000 wato MDGs cikin sauri. (Tasallah)