in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen BRICS sun kuduri kyautata hadin gwiwa a fuskar kiwon lafiya
2013-05-23 10:07:40 cri

Kasashen kungiyar BRICS, wato Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afirka ta Kudu sun dau alkawari cikin wata takardar bayan taron da suka yi a yayin taron majalisar lafiya ta duniya jiko na 66, wanda ke kankama a birnin Geneva, kasar Switzerland, cewar, za su kyautata hadin gwiwa tsakaninsu da kuma bunkasa kiwon lafiyar jama'arsu.

A fadin jawabin da aka baiwa kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua, kasashen kungiyar BRICS sun kuduri ci gaba da hadin gwiwa a harkar kiwon lafiya, kuma kan muhimman batutuwan lafiya guda 5, wato kamar bunkasa sa ido kan kiwon lafiya, da rage yawan hadarin cututtuka marasa yaduwa da dai sauransu.

Jawabin na mai ci gaba da cewar, kasashen 5 na kungiyar BRICS sun tattauna kan rahoton hukumar lafiya ta duniya (WHO) dangane da sa ido kan yadda ake tafi da muradun karni, inda suka lura cewa, duk da nasara da aka cimma, tsuguno bata kare ba muddin ana so a cimma buri nan da shekara ta 2015.

Kungiyar BRICS ta nanata kudurinta na ba da cikakken goyon baya ga hukumar lafiya ta duniya a matsayinta na hukuma dake lura da harkokin gudanar da batutuwan kiwon lafiya a duniya, tare kuma da ba da hadin kai ga jagora da hukumar ke yi da tsare-tsarenta, inda suka jaddada muhimmancin tabbatar da samar da kiwon lafiya mai inganci ga dukkan jama'a.

Wakilai kusan dubu 3 daga kasashe mambobin hukumar lafiya ta duniya guda 194 ne suka halarci taron na shekara-shekara.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China