in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci tallafin kudi don inganta harkokin kiwon lafiya a CAR
2014-03-19 09:46:41 cri

Majalisar dinkin duniya ta yi kiran da a hanzarta kara samar da tallafin kudade don inganta kayayyakin kiwon lafiya da ke kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR), ganin yadda kimanin rabi daga cikin wadannan kayayyakin sun lalace sakamakon yakin da ya wargaza kasar.

Kakakin kungiyar lafiya ta duniya (WHO) Tarik Jasarevic ya bayyana wa manema labarai a Geneva ranar Talata cewa, yayin da damina ke karatowa, hakan na iya kara haifar barazana ga bangaren lafiya na kasar.

Kungiyar lafiya ta duniya (WHO) da abokan huldarta sun himmatu wajen raba gidan sauro tare da samar da magani ga wadanda suka kamu da cutar zazzabin cizon sauro, cutar da ta kasance babbar annoba a kasar.

A karon farko kungiyar ta WHO ta zana dukkan cibiyoyin lafiyar da ke kasar, a matsayin wani muhimmin mataki na tunkarar duk wata matsalar lafiya da ta kunno kai a kasar cikin hanzari.

Kungiyar na bukatar dala miliyan 16.1 ne domin ta gudanar da ayyukanta na lafiya a kasar har zuwa watan Disamban shekarar 2014. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China