in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta amince da fahasar tattara bayanan kiwon lafiya da kwamfuta
2014-02-11 10:34:00 cri

Hukumomin kiwon lafiya na kasar Ghana za su shigar da wani tsarin kwamfuta wajen tsimi da tattara bayanai kan masu jinya, a wani labarin da kamfanin dillancin labarai na Ghana (GNA) ya rawaito a ranar Litinin.

Shirin nan zai baiwa likitoci da sauran ma'aikatan kiwon lafiya damar tattara duk wasu bayanai da suka shafi masu jinya ta hanyar fasahar zamani, kuma zai taimaka wajen ba da bayani kan cututtuka, tsara jadawalin tunatarwa da tsaida ranar zuwa asibiti, da tunatar da masu sayar da magunguna kan illar wasu magunguna suka iyar janyo masu fama da rashin lafiya, in ji GNA.

A lokacin da yake nuna yadda wannan na'urar take aiki a ma'aikatarsa a makon da ya gabata, ministan kiwon lafiyar kasar Ghana, Sherry Ayittey ya bayyana muhimmancin samun bayanai cikin kankanin lokaci kan maras lafiya da magunguna, ta yadda za'a iyar tabbatar da ba da jinya yadda ya kamata gare su.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya, ta nuna goyon bayanta kan shirin da aka yi masa taken 'Bayanan kiwon lafiya ta hanyar amfani da kwamfuta domin ba da magani da kulawa da kimanta tsaron lafiya'. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China