in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin za ta kaddamar da shirin kiwon lafiya na jama'a
2013-11-28 14:22:03 cri

Gwamnatin kasar Benin ta dauki niyyar kaddamar da wani tsarin kiwon lafiya na jama'a, da zummar kyautata daukar nauyin al'ummar kasar a fannin kiwon lafiya, in ji ministar kiwon lafiya ta kasar madam Dorothee Kinde Gazard a ranar Laraba a birnin Cotonou.

Wannan shirin kasa kan kiwon lafiyar jama'a zai taimaka wajen karfafa alfanun ayyukan jama'a na yanzu tare da amfanin da su yadda ya kamata, in ji jami'ar.

Da take magana a yayin taron kasa kan kiwon lafiyar jama'a, madam Gazard ta nuna damuwa cewa, rashin daidaici wajen samun jinya mai kyau na kasancewa daya daga cikin muhimman ayyuka a fannin kyautata tsarin kiwon lafiya na kasar Benin.

Duk da kyautata zahiri da aka samu a bangaren gine-ginen kiwon lafiya fiye da kashi 88 cikin 100 a shekarar 2011 a kasar Benin, amma jama'ar kasar da yawansu ya kai kashi 45,4 cikin 100 ne kawai ke amfani da su, a cewar madam Gazard.

Hakazalika jami'ar ta cigaba da nuna cewa, muhimman alkaluma na kiwon lafiya ba su gusa ba bisa wasu dalilai, misali, rashin ba da hadin kan al'umma wajen tantance su a gidajen likita da kasa warware matsalolinsu na rashin lafiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China