Annobar ta fada wassu unguwanni a sassa daban daban na jihar ,kamar yadda Abdulsalam Nasidi Darektan shirye shirye na sashin kula da yaduwar cututtuka na ma'aikatar kiwon lafiya na gwamnatin tarayyar kasar ya shaida ma manema labarai inda yace an samu rahoton wadanda suka kamu da cutar su 2,165 a wadannan wurare a jihar cikin watannin biyu da suka gabata.
Gwamnatin tarayya inji shi ta rigaya ta aike da wata tawaga zuwa jihar domin taimakawa magance wannan cuta sannan suka mika taimakon magungunan domin hana yaduwarta.(Fatimah Jibril)