Bisa labarin da aka bayar, an ce, ban da tura rukunonin likitoci zuwa kasashen waje, kasar Sin ta bayar da gudummawar na'urorin kiyon lafiya da magunguna, gina asibitoci da sauran cibiyoyin kiwon lafiya, horar da kwararrun kiwon lafiya, da kuma samar da kudi da fasahohi ga kasashe masu tasowa musamman kasashen Afirka. Kana Ren Minghui ya nuna cewa, a cikin 'yan shekarun nan, an fadada hadin gwiwar dake tsakaninsu zuwa fannonin yaki da zazzabin cizon sauro, kula da lafiyar mata da yara da dai sauransu.
Ren Ming Hui ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kungiyoyi, asusu da kuma kamfanoni da su shiga a dama da su, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da sauran abokan hulda da kungiyoyin kasa da kasa, da kuma daukar sabbin matakai wajen sa kaimi ga yin hadin gwiwa a bangaren kiwon lafiya a tsakaninta da kasashen Afirka. (Zainab)