in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 6 sun rasu a sanadiyyar fashewar boma-boman da aka dasa cikin mota a Afghanistan
2013-11-17 17:03:15 cri
Ran 16 ga wata, kakakin ma'aikatar kula da harkokin aikin gida ta kasar Afghanistan Seddiq Seddiqi ya bayyana cewa, a wannan rana, mutane 6 sun rasu, yayin da wasu 22 suka jikkata a sanadiyyar fashewar boma-boman da aka dasa cikin wata mota a wata tashar bincike dake yammacin birnin Kabul. Kuma ya zuwa yanzu, babu wata kungiyar data dauki alhakin wannan hari.

Bugu da kari, nisan da ke tsakanin inda boma-bomai suka tashe da wurin da za a gudanar da taron Loya Jirga bai kai mita dari ba. A mako mai zuwa, manyan shugabanni na siyasa da na kabilu za su yi taron a nan wurin, don yin shawarwari kan harkokin yarjejeniyar tsaron dake tsakanin kasashen Afghanistan da Amurka.

Tun watan Nuwamba na shekarar da ta gabara, an fara yin shawarwari kan yarjejeniyar tsaron dake tsakanin kasashen biyu, inda suka tattauna kan manyan batutuwan da suka hada da yawan sojojin kasar Amurka da za su ci gaba da zama a kasar Afghanistan bayan kungiyar NATO ta janye sojojinta daga kasar da dai sauran batutuwa. Kuma a halin yanzu, kasashen Amurka da Afghanistan sun riga sun cimma ra'ayi daya kan harkokin daftarin yarjejeniyar, kuma za a ci gaba da tattaunawa kan daftarin yayin taron Loya Jirga. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China