Sufeto janar na sandar kasar Kenya, David Kimaiyo, ya bayyana cewa dukkan hedkwatocin 'yan sandar sun samu umurnin karfafa matakan tsaro a cikin manyan biranen kasar.
A ranar 21 ga watan Satumban shekarar 2013, wasu mutane dauke da makamai sun kutsa kai a cikin cibiyar kasuwancin Westgate kana suka afkawa mutanen dake cikin wannan ginin wuta. A cewar mista Kimaiyo, 'yan sandar yankin dake makwabtaka da Somaliya sun karfafa yin sintiri. A Mombasa, birni mafi girma na biyu dake kudu maso gabashin kasar, hukumomin wurin sun tabbatar da cewa birnin na cikin shirin ko ta kwana mafi girma.
"Na ba da umurni ga manyan ofisan 'yan sanda domin tabbatar da tsaro yadda ya kamata a Mombasa da kuma kewayenta", in ji Komandan 'yan sandan Mombasa, Robert Kitur a cikin wata hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Nairobi, Mombasa da wasu sauran birane na kasar Kenya, suna fuskantar hare-haren ta'addanci tun lokacin da kasar ta tura sojojinta a kasar Somliya a karshen shekarar 2011 domin yaki da mayakan kungiyar Al-Chabaab. (Maman Ada)