in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Liberia da Saliyo
2014-08-18 10:33:48 cri
A ranar 16 ga wata, gwamnatin kasar Kenya ta ba da sanarwar hana fasinjoji daga kasar Guinea, Liberia da Saliyo wadanda ke fama da cutar Ebola mai tsanani shigo wa kasar. Haka kuma kamfanin jiragen saman kasar ta Kenya ya tsaida kuduri a wannan rana, cewar tun daga ranar 20 ga wata, za a dakatar da zirga-zirgar dukkan jiragen sama daga kasar Kenya zuwa kasashen Liberia da Saliyo.

Hakazalika, kasashen da ke yankin gabashin Afirka suna sa ido sosai tare da daukar matakan gaggawa don hana cutar ta Ebola shiga cikin kasashen da ke yankin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China