Wata sanarwa da ofishin na UNEP ya fitar ta ce ya yin taron dake tafe a ranar Talata mai zuwa, kwararrun za su tattauna kan wasu sabbin fasahohi, da ake fatan za su rage tsadar samar da tsaftacaccen ruwan sha da kimanin kaso 50 bisa dari, ga mazauna yankunan karkara a Kenya.
Kaza lika sanarwar ta bayyana babban shirin hadin gwiwar sassan game da kare muhalli, a matsayin abin da zai zamo jagoran cimma nasarar shirin kyautata tsimin ruwan sama da ake gudanarwa a kasar ta Kenya.
Har wa yau karkashin wannan shiri na kare muhallin halittu, ana sa ran kwararru daga Sin za su baiwa daruruwan jama'ar nahiyar Afirka horo, game da hanyoyin rage tsadar gudanar da ayyuka, da tattalin filaye da kuma dabarun noman rani. (Saminu Alhassan)