A yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana daukar kasar Afirka ta Kudu a matsayin kasar ketare da ta fi son zuba jari, kuma Sin na sa kaimi da kuma nuna goyon baya ga manyan kamfanonin kirar na'urori na kasarta da sauran kamfanoni masu bunkasa cikin sauri da su je kasar Afirka ta Kudu domin taimakawa wajen ciyar da harkokin masana'antun kasar gaba. Haka kuma, ana son habaka gamayyar moriyar kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu, da kuma ciyar da kokarin dunkulewar kasashen Afirka gaba. Bugu da kari, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka wajen ci gaba da ba da gudumawa kan yaki da cutar Ebola.
A nasa bangare kuma, shugaba Jacob Zuma ya ce, kasarsa na son karfafa shawarwari da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin kan fannonin siyasa, tattalin arziki da cinikayya, albarkatun teku, al'adu da dai sauransu. Kuma kasashen Afirka na maraba da taimakon kasar Sin na samar da kayayyakin more rayuwa, ciyar da yunkurin dunkulewar nahiyar gaba, domin taimaka wa kasashen Afirka wajen cimma burinsu na neman bunkasuwa. (Maryam)