in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu na kan hanyar kaiwa ga cimma kudurorin ci gaba na MDGs
2014-09-22 12:25:05 cri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya ce, Afrika ta Kudu ta yi aiki tukuru a fafutukar da take yi na kaiwa ga cimma kudurorin ci gaba na wannan karnin MDGs, kuma kasar za ta ci gaba da kokari domin ganinta cimma ruwa a game da nasarorin da ake bukata, kamin karshen wa'adin shirin, wanda za'a dakatar da shi a shekara ta 2015.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da yake kan hanyarsa zuwa New York, domin halartar zaman babban taron MDD, kashi na 69, wanda ke da nufin tattaunawa a kan gurgusowar karshen wa'adin cimma nasarorin kudurorin wannan karnin da kuma ajandar ci gaba ta duniya a bayan shekara ta 2015.

Zuma ya ce, shirin ya samu nasara a Afrika ta Kudu a yayin da aka samu nasarar rage adadin mutanen da suke dogara da dala 1.25 a ko wace rana, da kusan rabi bisa dari, kuma an samu nasarar rage adadin masu fama da matsalar yunwa da rabi bisa dari.

Zuma ya yi nuni da cewar, kasar ta Afrika ta Kudu ta samu galabar cika hakkoki na cimma kuduri na 2, na samar da kafofin ilmin firamare ga daukacin al'ummar kasar, kuma kasar na iyakacin kokarinta wajen ganin tallafa wa matan kasar wanda ya yi daidai da cimma manufa ta 3 ta kudurorin wannan karnin.

Shugaban kasar ta Afrika ta Kudu ya ce, kasarsa ta samu gagarumin ci gaba a fannin kiwon lafiya. Zuma ya kara da cewar, an samu gagarumin ci gaba a wajen cimma kuduri na 4 a yayin da Afrika ta Kudun ta samu nasarori wajen inganta bangaren kula da lafiyar mata da kuma rage adadin yaran dake mutuwa, sai dai ya ce, har yanzu akwai bukatar sadaukar da kai domin kara samun nasara da ake bukata. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China