Mr Qin ya bayyana hakan ne dangane da matsayin kasar akan tambayar da manema labarai suka mashi kan kin amincewar da gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi na hanaga yunkurin neman samun takardar shiga kasar ta gada Dalai Lama ya yi, domin kauracewa mummunan tasiri ga huldar dake tsakaninta da Sin.
Mr Qin ya bayyana cewa, Dalai Lama dan gudun hijira ne dake yunkurin kawo barakahaifar da illa ga cikakken yankin kasa da ikon mulkin kasar Sin da kuma hadin kan al'ummomin kasar ta hanyar amfani da addini, a don haka, Sin bata amince da kokarin Dalai Lama ba wajen kawo mummunan mummunar baraka ga kasar Sin a kasashen waje ta kowace hanya.(Fatima)