Kamfanin Zendai dake Shanghai a nan kasar Sin, wanda ya kware a fannin ginin gidaje ya yi alkawarin zai baiwa 'yan kasar Afrika ta Kudu wata dama ta yin aiki tare, a karkashin wani aikin gidaje da kamfanin zai yi a Afrika ta Kudu, wanda darajarsa ta kai mizanin rand din Afrika ta Kudu, biliyan 84, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 7.7.
A yayin da yake jawabi a dandalin wani taro da aka shirya tsakanin Afrika da kasar Sin a birnin Johannesburg, babban jami'in gudanarwa na kamfanin, Wenhui Du ya ce, aikin da za su yi a Afrika ta Kudun zai kunshi ginin gidaje kusan dubu 100, a wani wuri mai fadin hekta dubu 1 da dari 6, wanda za'a kawata da manyan kantunan sayar da kayayyaki, da filin wasanni, da makarantu da wuraren hutawa da wata cibiyar al'adu.
Du ya ce, kamfanin zai dauki tsawon shekaru 15 zuwa 20 kamin ya kammala aikin wanda ake sa ran zai haifar da ayyukan yi kusan dubu 200 kuma ana sa rai ginin zai janyo saka jari daga kasashen ketare. (Suwaiba)