in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Afirka ta Kudu za su baje kolin kayayyakinsu a Sin
2014-10-14 10:32:03 cri

Ministan cinikayya da masana'natu na kasar Afurka ta Kudu Rob Davies ya bayyana cewa, kamfanonnin kasar 31 za su baje kayayyakin su a kasar Sin daga ranar 20 zuwa 31 ga watan Oktoba, a wani bangaren na murnar kulla huldar diflomasiya tsakanin kasashen biyu.

Ministan wanda ya bayyana hakan ranar Litinin ya ce, kasarsa za ta yayata muhimman ayyukanta na zuba jari da fitar da kayayyaki a biranen kasar Sin da suka hada da Hong Kong, Shenzhen, Chengdu, Shanghai da kuma Beijing.

Bugu da kari Afirka ta Kudu za ta shirya wasu shugulgula da suka hada da na bunkasa al'adu, nuna fasahohin hannu, baje kolin kayayyaki, bincike da musayar ilimi a Sin, yayin da ita ma kasar Sin za ta gabatar da nata kayayyakin, yayata wa da kuma musayar shagulgula a kasar Afirka ta Kudu.

A cewar ministan, kayayyakin da kasarsa ke fitar wa zuwa kasar Sin sun hada da kayayyakin da ake hako wa, tama da karafa, sinadarai da darajarsu ta kai dala biliyan 5 a shekara, yayin da ita kuma Afirka ta Kudu ke shigo da tufafi, injuna, akwatunan talabijin, kayayyakin sadarwa, tebura, kujeru a gadaje, da kuma takalma daga kasar Sin.

Davies ya ce, Afirka ta Kudu ta shiga yin hadin gwiwa da Sin ne bisa manyan tsare-tsare da nufin bunkasa dangantakar da ke tsakaninsu a fannin siyasa, tattalin arziki, kuma Afirka ta Kudu tana son inganta dangantakar cinikayya da ke tsakanin kasashen biyu a halin yanzu.

Kasar Afirka ta Kudu tana bikin cika shekaru 16 ne da kulla huldar diflomasiya tsakaninta da kasar Sin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China