in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu na martaba kawancen dake tsakaninta da Sin, in ji ministan cinikayya
2014-11-28 10:14:00 cri

Ministan ma'aiakatar cinikayya da masana'antun kasar Afirka ta Kudu Rob Davies ya ce, kasarsa na matukar martaba kawancen dake tsakininta da kasar Sin, wanda ya ce, ya bude wa Afirka ta Kudun sabbin hanyoyin samun ci gaban tattalin arziki masu yawa.

Davies wanda ya bayyana hakan a birnin Cape Town, yayin wani taron ganawa da 'yan jaridu, ya kara da cewa, kasashen biyu na ci gaba da kokari wajen tinkarar kalubalolin dake fuskantar kasashe mambobin kungiyar hadin kan yankunan kudanci karkashin inuwar kungiyar BRICS, da ma ta sauran hanyoyin da suka dace.

Ministan harkokin cinikayyar ya kuma ce, domin karfafa dangantakar sassan 2, shugaba Jacob Zuma ya shirya ganawa da shugaban kasar Sin Xi Jinping cikin wata mai zuwa a birnin Beijing, ganawar da za ta ba su damar yin musayar ra'ayoyi, domin karfafa dangantakar kasashen nasu. Kaza lika ana sa ran tattauna muhimman batutuwa game da fadada hadin gwiwa ta fuskar cinikayya da zuba jari tsakanin kasashen biyu.

A cewar Davies, hada-hadar kasuwanci tsakanin kasashen biyu na matukar karuwa tun daga shekarar 2008. Inda ya zuwa karshen shekarar 2013, yawan kudaden cinikayyar sassan biyu ya daga daga dalar Amurka kusan biliyan 11, ya zuwa dala biliyan 25. Matakin da kuma ya sanya kasar ta Sin kasancewa abokiyar cinikayya mafi girma ga Afirka ta Kudun a nahiyar Asiya da ma duniya baki daya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China