A halin da ake ciki, ministar kwadago ta kasar Afrika ta Kudu Mildred Oliphant, ta gana da Mr. Yin Weimin, shugaban ma'aikatar albarkatun jama'a da tsaron jin dadin rayuwar kasar Sin a birnin Cape Town na kasar Afrika ta Kudu, domin tattaunawa a kan batutuwa da suka hada da kara darajar albarkatun jama'a ta hanyar horo, da kuma maganar samar da kafofi na ayyukan yi.
Wata sanarwa wacce ta fito daga gwamnatin Afrika ta Kudu ta ce, a karshen taron bangarorin biyu, sun amince da tashi haikan, domin tabbatar da kasashen biyu sun rattaba hannu a kan amincewa da yarjejeniyar aiki tare, da zimmar bunkasa manufofin raya kasa, tare da kara karfafa bincike daga bangaren kwadago da kuma sauran bangarori.
Yin, ya ce, ziyararsu na da muradin ganin an samu kafuwar musayar albarkatun jama'a, da kuma samar da guraben ayyukan yi tsakanin Afrika ta Kudu da kasar Sin, musamman ma kamar yadda Yin ya ce, ita ma kasar Sin na fama da kalubale na matsalar ayyukan yi, to sai dai ya ce, tuni kasar Sin ta dauki matakai na magance matsalolin.
A jawabinta, ministar kwadago ta Afrika ta Kudu ta ce, kasashen biyu na fuskantar kalubale na matsalar aikin yi a bangaren matasa, kuma kamar yadda ta ce, wanan matsala ce da ta shafi kasashen duniya baki daya, to sai dai ta ce, Afrika ta Kudun na daukar matakai na magance matsalar. (Suwaiba)