A ranar Asabar ne kasar Afirka ta Kudu ta bi sahun sauran kasashen duniya a kokarin da ake na wayar da kan jama'a wajen kare namun dajin da ke daf da bacewa a doron kasa irin su giwaye da karkanda da kuma zakuna.
Ministar kula da muhallai na kasar Afirka ta Kudu madam Edna Molewa ta jagoranci wani macin da dubban 'yan kasar ta Afirka ta Kudu suka shirya a biranen kasar kimanin 18 ciki har da Pretoria, a wani mataki na fadakar da jama'a muhimmancin kare namun daji.
Baya ga kasar Afirka ta kuDu, an kuma gudanar da irin wannan maci a kasashen Afirka 36 da wasu kasashe 134 na duniya a kokarin da ake yi na kare giwaye da karkanda da kuma zakuna daga bacewa.
Ministar ta yi kira ga jama'a da al'ummomi musamman wadanda ke kewaye da karkanda, da su shiga cikin wannan yaki da farautar namun dajin da ke kokarin bacewa.
Shi dai wannan maci da aka shirya ya aike da wani sako mai karfi ga wadannan kasashe da su bullo da dokoki masu tsauri kan wadanda aka kama da laifin farauta ko fataucin namun daji.
Ita ma gwamnatin kasar Afirka ta Kudu tana shirin yi wa nata dokokin da suka shafi farautar giwaye da karkanda gyaran fuska, ta yadda za a sanya hukunci mai tsanani kan wadanda aka samu da laifin fataucin namun daji.(Ibrahim)