Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaran sa na kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, a jiya Litinin a birnin Fortalezan kasar Brazil.
Lokacin da suke ganawa shugaba Xi ya bayyana cewa, yayin ziyarar sa a Afirka ta Kudu a bara, an cimma matsaya game da daga matsayin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ya zuwa wani tushe, kuma muhimmin aiki da ya dara saura a fannin manufofin diplomasiyyar bangarorin biyu. Kaza lika an cimma daidaito kan batun kara hadin gwiwar kasashen biyu a dukkan fannoni.
Har wa yau shugaban kasar ta Sin ya ce cikin kankanen lokaci, an riga an aiwatar da manufofi da dama da kasashen biyu suka tsara, an kuma cimma nasarori da dama a fannin hadin gwiwarsu sakamakon himmar kasashen, lamarin da ke sa kaimi ga kasashen biyu wajen cimma moriyar juna da bunkasuwa tare.
Hakazalika kuma Xi Jinping ya nuna cewa, zaman lafiya da bunkasuwa, sun zama abubuwa masu muhimmanci matuka ga nahiyar Afirka. Kuma kasar Sin tana fatan more fasahohin samun bunkasuwa tare da kasashen Afirka, tare da shiga harkokin kiyaye zaman lafiya a nahiyar, da bada himma wajen gudanar da ayyukan nahiyar a fannin hadin gwiwar kasa da kasa da yankunan nahiyar. Bugu da kari Xi ya ce Sin na fatan bada babbar gudummawa wajen dunkulewar Afirka.
A nasa bangare, shugaba Zuma ya bayyana cewa, kasarsa tana gaggauta raya masana'antu da tattalin arziki, tare da kokarin bunkasa yanayin zaman lafiya da lumana da kuma bunkasuwar nahiyar Afirka baki daya. Ya ce yana fatan kara inganta dangantakar abokantaka tsakanin Afirka ta Kudu da kasar Sin, tare da cimma matsaya kan manyan batutuwan kasa da kasa da yankuna, da kuma fadada hadin kan su a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da makamashi da dai sauransu.
Ana dai sa ran gudanar da taron ministoci na dandalin tattaunawa, kan hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a shekarar 2015 a kasar Afirka ta Kudu, taron da Afirka ta Kudun ke fatan zai ba ta damar daga matsayin dangantaka da hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka baki daya. (Zainab)