An dai gudanar da bikin kaddamar karbar dabbobin ne, da ba da kariya gare su, a wani wuri dake kusa da dakin dorinar dajin dake gidan ajiye namun dajin.
Yayin bikin, mukaddashin jakadan ofishin jakadancin Sin a kasar, Yang Yirui ya bayyana cewa, a yayin da shugaba Zuma ke ci gaba da ziyarar aiki a kasar Sin, bangarorin biyu za su rattaba hannu kan jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa, ciki har da ba da kariya ga dabbobin daji.
Mr. Yang ya kara da cewa makasudin karbar rikon dorinar dajin da ofishin jakadancin Sin ya yi shi ne, kokarin ba da gudummawa a wannan fanni, tare da sa kaimi ga jama'a wajen shiga wannan aiki gwargwadon iko.
Yang ya kara da cewa, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci sosai kan kiyaye dabbobin daji, inda ta fidda jerin dokoki, da kafa tsarin gudanar da aiki tsakanin hukumomi bisa doka, da kafa rukunin musamman na yaki da sace ko farautar dabbobi, domin yaki da fasakwaurin sassan jikin dabbobin daji, da cinikayyarsu ba bisa ka'ida ba, ta yadda za a kai ga dakile ayyukan keta dokoki cikin hadin gwiwa.(Fatima)